Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour a zaben 2023 Peter Obi ya bayyana cewa bai taba yin magudin zabe ba, ko kuma tayar da hankali, ta wata hanya a siyasa a tsawon lokutansa a cikin sha’anin siyasa.

Obi ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, inda ya sake jaddada kudurinsa na yin siyasa mai tsafta da bin doka.

Peter Obi ya kara da cewa bai taba yin wani yunkuri ba na sace akwatunan zabe, ko yunkurin yin magudi, ko kuma daukar batagari don tayar da hankula a gurin zabe.

Acewarsa a ko da yaushe ya kasance mai mutunta abokan hamayyarsa a siyasan, tare da tabbatar da cewa babu wanda ya yi takara da shi da za a ci masa mutunci ko tauye masa hakkinsa.

Obi ya kuma yi watsi da cewa yana da burin samun mulki, yana mai cewa burinsa shi ne ci gaban kasa, ba burin kansa na samun mulki ba.

Obi ya ce burinsa shine a yanzu na ganin Najeriya ta gyara, tare da magance cin hanci da rashawa da kuma da kuma tabbatar da doka da oda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: