Shugaban Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC Ola Olukoyede, ya ce mafiya yawan gidajen da aka yi watsi da su a babban birnin tarayya Abuja mallakin ma’aikatan gwamnati ne da suka aikata almundahana.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a Abuja a jiya Laraba, a gurin wani taron tattaunawa mai taken Mahimman batutuwan da suka shafi muhalli na gidaje na Najeriya.
Shugaban ya ce an yi watsi da wasu daga cikin kadarorin sama da shekaru Gom, inda ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kafa wani kwamiti na musamman da zai yi aikin fara ziyartar irin wadannan guraren.

Olukayode ya ce kwamitin ba iya Abuja kadai zai gudanar da aikin sa ba, harma da sauran sassan Kasar, don gano wadanda suka mallaki kadarorin.

Ya ce bayan kammala bincike za su tabbatar da ganin sun dauki matakin da ya dace akai.
Ayayin jawabin shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa NBA fam Osigwe, ya ce akwai bukatar a samar da tsarin da zai inganta tabbatar da mallakar kadarori a Njeriya.
