Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahya ya rattaba hannu akan dokar da za ta samar da sabbin kananan hukumomi 13, kari akan Kananan hukumomi 11 da ake da su a Jihar, tare da kara yawansu zuwa 24.

Gwamna Yahya ya ce matakin nada nufin gyara rashin daidaito, a tsarin mulkin kananan hukumomi, dorewar kuɗi, da manufofin siyasa.
Gwamnan ya sanya hannu akan dokar ne tun a ranar 25 ga watan Agustan da muka yi bankwana da shi, bayan zaman jin ra’ayoyin jama’a da aka yi kan samar da karin sabbin kananan hukumomi a Jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Isma’il Uba Misalli ya fitar, ya ce an yi saurin amincewa da kudirin ne bayan yin karatu na daya da na biyu da sauraren ra’ayoyin jama’a da kuma karatu na uku, daga bisa majalisar dokokin jihar ta amince da shi.

A jawabisa gwamna Yahaya ya ce sabbin Kananan hukumimun sun samu amincewa ne daga sashe na 4(7) na kundin tsarin mulkin Kasa, da ya bai’wa majalisun Jihohi ikon samar da dokokin tabbatar da zaman lafiya, da tsari da shugabanci nagari, kuma zai samar da ci gaba ga mutanen da abin ya shafa da ma Jihar baki daya.
