Gwamnatin Jihar Binue ta haramta gudanar da bukukuwan yaye dalibai a makarantun Firamare, da makarntun renon yara, Nursery a jihar.

Mukaddashiyar kwamishiniyar ma’aikatar ilimi ta Jihar Helen Nambativ, ce shaidawa kamfanin dillancin labarai na Kasa a yau Talata a garin Makurdi babban birnin Jihar.

Gwamnatin ta ce dukkan makarantun da aka kama da karya dokar za a rufe su na wani lokaci, bisa tsarin ilmi da ya haramta gudanar da bikin.

Kwamishinar ta kuma ce gwamnatin ta samar da dukkan hanyoyin da ake bukata domin aiwatar da sabon tsarin.

Ta ce sabuwar manufar da ta fara aiki nan take, ba wai kawai ta shafi iya mutane ba ce, za ta kuma tsaftace fannin ilimi a matakin farko.

Sannan matakin zai kuma ragewa iyaye kashe kudi, da kuma mayar da hankali kan ci gaban ilmin ‘ya’yansu.
Ta kuma bayyana cewa za a kafa rundunar da za ta yi aikin tabbatar da ganin an bi dokar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: