Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta kasa sun goyi bayan shirin fara jarabawar Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma WAEC da na’urar kwamfuta a Ƙasar.

A baya hukumar WAEC ta bayyana shirinta na fara jarrabawar ta hanyar na’urar kwamfuta daga shekarar 2026.

Sai dai a yayin da yake jawabi ga ‘yan majalisar dokokin kasar da masu ruwa da tsaki a wani taron wayar da kan jama’a a Abuja, Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya ce amfani da kwamfuta wajen yin jarrabawar a Najeriya, zai karfafa tare da sauya fasalin tsarin tantance dalibai a fannin ilimin Ƙasar.

Alausa ya ce gwamnatin tarayya na goyon bayan gudanar da jarabawar WAEC ta hanyar a na’ura mai kwamfuta domin kawar da kura-kuran jarabawar da ake samu.

Ministan ya ce a cikin cibiyoyin da aka kebe na kwamfuta zai rage tafka kura-kurai matuka, tare da kare sahihancin jarrabawar da ake yi, hakan kuma zai kara daukaka martabar jarabawar da ake yi a gida da waje.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: