Majalisar wakilan Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ake yadawa cewa ‘yan majalisar na shirin kalubalantar shugaban majalisar Tajudeen Abbas bayan kammala hutun da yayi.

Mataimakin shugaban Majalisar Hon Philip Agbese ne ya musanta batun a yau Talata, a ganawarsa da manema labarai a Abuja.
Ya ce bayan hutun Tajudden mambobin majalisar sun ci gaba da gudanar da ayyukansu bisa hadin kai, sannan kuma sun amince da shugabancin Tajuddeen.

Kalaman na Agbese na zuwa ne biyo bayan wani rahoto da aka yada cewa ‘yan majalisar sun nuna rashin gamsuwa da ayyukan mazabu da ba a biya ba, da wasu ayyuka da aka dakatar da ‘yan majalisar daga aiwatarwa, wanda hakan ke yunkurin haifar da barazanar da rashin nuna goyan baya ga shugaban majalisar.

Sannan rahotannin sun ce ‘yan majalisar sun zargi shugabannin cikinta da mayar da ‘yan majalisar baya, bayan da suka gano cewa an dauki sabbin ma’aikata 785 ba tare da saninsu ba.
To sai dai Agbese ya yaba da jagorancin shugaban majalisar, bisa adalcinsa da kuma jajircewa wajen kyautata jin dadin ‘yan majalisar da ci gaban mazabu, inda ya bayyana rahotannin a matsayin yunkurin haifar da sabani a zauren majalisar.
