Kungiyar tuntubar ma’aikata ta Najeriya NECA ta ce gwamnatocin jihohi ba su da wani uzuri na kin biyan ma’aikatan gwamnati sama da Naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Shugaban kungiyar Adewale Smatt-Oyerinde ne ya bayyana hakan a yau Talata a hirarsa da Channels Tv, ya ce karin kudaden shiga daga asusun gwamnatin tarayya ya rage cece-kuce game da gazawar wasu jihohi.

Acewarsa babu wata Jiha da ta ke da uzuri a halin yanzu da za ta ci gaba da biyan naira 70,000, a matsayin mafi karancin albashi musamman ga mutanen da ke fama da tsadar man fetur, yayin da jihohi da dama ke ci gaba da aiki da motocin CNG, yana mai cewa akwai bukatar a kara kaimi akai.

Ya ce dukkan wani mataki da aka dauka na rage radadin ma’aikata, a matsayinsu na masu tafiyar da harkokin tattalin arzikin Kasa zai bunkasa ayyukansu.

Ya ce yana da kyau gwamnatocin jihohi su dauki ma’aikatan gwamnati a matsayin ginshikanta wajen gudanar da ayyukanta.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: