Hukumar binciken Tsaro ta Kasa NSIB ta ce mutane 12 ne suka jikkata daga cikin fasinjoji 583 da ke cikin jirgin Kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.

Hukumar ta bayyana hakan ne a yau Talata, a lokacin da darakta Janar na hukumar Kyaftin Alex Badeh ke bayar da bayanai kan binciken da gudanar bayan kauce hanya da wani jirgi ya yi.
Badeh ya ce an nada wani mai bincike IIC da zai jagoranci binciken, tare da yin aiki tare da masu ruwa da tsaki, ciki har da Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya NRC.

A cewarsa hukumar ta riga da ta dauki matakan kariya, kamar tabbatar da wurin da kuma adana muhimman bayanai, ciki har da kwamarar tsaro ta CCTV da sauran kayan da za su taimaka wajen gano musabbabin karkacewar jirgin.

Badeh ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da su magance matsalar karancin kudade domin inganta aikin ofishin na gudanar da cikakken bincike da kuma kare rayukan ‘yan Najeriya.
Kazalika ya ce hukumar za a fitar da rahoton karshe cikin kwanaki 30 na faruwar lamarin, tare da bayar da shi ga hukumar ta NRC, da hukumomin gwamnati, da sauran jama’a.
Idan baku manta ba lamarin ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata a lokacin da jirgin ke kan hanyar Kaduna daga Abuja, jim kadan bayan tasowarsa da misalin karfe 11 na safe.
