Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce bai yi nadama ba wajen zaben Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa ba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa a ranar Talata na taya murna ga Shettima bisa cikarsa 59 a duniya.
Shugaban ya bayyana Shettima a matsayin ɗan uwan, abokin tarayya, kuma amintaccen mataimakinsa.

Shugaban ya ce Shettima dan kishin dimkuradiyya ne, da shugabanci nagari, habaka tattalin arziki, inda ya bayyana cewa hazakarsa, biyayyarsa, da goyon bayansa a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, ya kara karfafa kudurin gwamnatin tarayya na ganin ta cimma burinta na sabunta fata.

Tinubu ya kuma sake yabawa Shettima bisa nagartarsa wajen ganin Najeriya ta ci gaba, tun daga kan matakin gwamna da yayi a Borno da kuma Sanata da zama har kawo wannnan lokacin.
A gebe guda kuma shugaban ya taya gwamnan jihar Zamfara Dr Dauda Lawal murnar cika shekaru 60 a duniya.
Shugaba Tinubu ya yabawa Lawal bisa jajircewarsa na ci gaban jihar Zamfara da kuma jajircewarsa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
