Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu zai magance kashi 80 cikin 100 na matsalolin gidaje da alkalai ke fuskanta a Najeriya.

Wike ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da wata kotun majistare a Abuja a yau Talata, inda ya bayyana cewa za a mika rukunan guda 50 ga babbar kotun birnin tarayya a watan Yulin shekarar 2026 mai zuwa.

Ya bayyana cewa yayin da kotun za ta karbi rakuni 20 a watan Oktoba 2025, inda kuma za a mika rakuni 30 a watan Yuni 2026 ga babbar kotun tarayya.

A cewarsa lamarin ya shafi alkalan da ke zaune a matsayin masu haya don tabbatar da walwalarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: