Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya dora wa majalisar gudanarwar jami’ar Kashim Ibrahim alhakin bunkasa al’adun gudanar da bincike mai zurfi, da kirkire-kirkire domin samun damar shawo kan kalubalan da ke tattare a kokarin da ake yi na dawo da zaman lafiya a Jihar.

Gwamnan ya yi kiran ne a jiya Litinin a lokacin da ya ke kaddamar da jagora da kuma shugaban Majalisar Dr Muhammadu Indimi da mambobin Majalisar gudanarwar Jami’ar a zauren Majalisar na gidan gwamnatin Jihar da ke Maiduguri.
Ya kara da cewa kaddamar da Jami’ar wani bangare ne na kokarin mayar da Jami’ar a matsayin fitilar ilimi, kirkire-kirkire da kuma da’a, ba wai kawai ga Arewa maso Gabas ba, har ma da Najeriya baki daya.

Gwamna Zulum ya bayyana jin dadinsa bisa ci gaban da aka samu na karin dalibai daga 300 zuwa 10,000 a cikin shekaru shida da suka gabata.

Zulum ya kuma umarce da su bayar da fifiko ga jindaɗin ma’aikata da ɗalibai, da kuma kare muradan jami’ar don sanya ta a alkiblar da ta dace.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa gwamnatin sa na bayar da jarin da ba a taba ganin irinsa ba a fannin ilimi, ya gina sabbin manyan makarantu 139, ya gyara wasu da dama tare da daukar dubban malamai.
Sannan ya taya su murna bisa mukaman da suka samu.
A nasa jawabin Indimi ya ce ya amince da mukamin, tare da bayar da hadin kai ga Jihar, da kuma mataimakansa don ganin an samu sauye-sauye masu inganci a Jami’ar.
