Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da yin watsi da yankin Arewa ta tsakiya bisa yawaitar kashe-kashe da ake samu a yankin.

A wata wallafa da Atiku ya fitar, ya ce rashin tsaro ya kara kamari a jihohin Arewa ta Tsakiya, wanda hakan ya fito da gazawar gwamnatin karara wajen gaza kare ‘yan kasarta.
Ya ce Sakamakon kashe-kashen da ake yi a yankin Arewa ta Tsakiya hakan ya nuna karara cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da yankin da zubar da jinin da ake yi.

Acewarsa a baya Jihar Kwara na zaune lafiya, a halin yanzu ta zama cibiyar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, yayin da jihar Neja kuwa ‘yan bindiga na kai hari a sansanonin soji, suna kashe sojoji, har ma da kashe masu ibada a masallaci.

Alhaji Atiku ya kara da cewa Jihar Filato da Benue ana ci gaba da kashe mutane, inda ya ce gwamnatin tarayya ta ki kulawa da hakan.
Atiku ya ce ya zuwa watan Mayu shekara nan, an samj asarar rayuka sama da 10,000 a jihohin Arewa, inda ake zargin Benue ce ta fi samun fiye da rabin wadanda suka mutu, ya kuma yi gargadin cewa ana ci gaba da kashe dimbin jama’a a mako-mako tun daga lokacin.
Atiku ya bayyana lamarin a matsayin gazawa mai girma a aikin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Atiku wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya ci gaba da zargin jam’iyyar APC mai mulki da mayar da hankali wajen yaki da ‘yan adawa maimakon tabbatar da tsaro a Kasar.
