Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ce layin dogo na Legas ya yi jigilar fasinjoji sama da miliyan biyar cikin shekaru biyu da kaddamar da shi.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa a yau Laraba, ya bayyana cewa, jirgin kasa ya yi aiki ba tare da wani hadari ko daya ba tun bayana fara aiki.

Sanarwar ta ce a cikin wadannan shekaru biyun jiragen kasa na gudu kowane minti 10, suna yin tafiye-tafiye sama da miti 90 a kowace rana.

Gwamnan ya ce waɗannan nasarorin sun nuna cewa idan aka yi aiki tare da sadaukarwa da manufa, za a iya gina tsarin da ake bukata.

A yayin bikin cika shekaru biyun gwamnan ya sanar da rage kashi 50 cikin 100 na farashin jirgin daga a gobe Alhamis,4 ga watan Satumba.

Gwamnan ya kaddamar layin ne a shekarar 2023, a wani bangare na kokarin da jihar ke yi na fadada zirga-zirgar ababen hawa da saukaka cunkoson ababen hawa a cikin birnin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: