Ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta sanar da shiga tsakani cikin gaggawa kan lalacewar da bangaren gadar Shagamu zuwa Benin, inda ta bayar da tabbacin samun mafita cikin gaggawa ga masu amfani da hanyar.

A wata sanarwa mai dauke da sanya hannun mai bai’wa Ministan ayyuka shawara na musamman David Umahi shawara na muhamman Uchenna Orji ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce ma’aikatar na ci gaba da bin diddigin gyare-gyaren tare da tura tawagar injiniyoyi zuwa wurin da gadar ta lalace da ke kan iyakar jihohin Edo da Ondo a hanyar Shagamu zuwa Benin.

Sanarwar ta ce za a dauki tsawon kwanaki 45 bayan aikin zuba kankare don ci gaba da zirga-zirgar ababen hawa a bangaren titin domin bai’wa aikin damar bushe.

Ministan ya kuma nemi afuwar masu amfani da hanyar a kan matsalolin da suka fuskanta ko kuma za su fuskanta a lokacin aikin gyaran.

Ya bayar da tabbacin cewa ma’aikatar ayyuka ta tarayya za ta hada kai da jami’an hukumar kiyaye haddura ta tarayya wajen kula da zirga-zirgar ababen hawa a bangare daya na gadar a tsawon lokacin gyaran don gudun kada masu ababen hawa su makale a cikin cunkoson ababen hawa.

Ya jaddada cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya baki a kan gyaran gadoji sama da 30 a fadin kasar nan a shekarar 2025 kadai, kuma za a gudanar da gyaran cikin gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: