Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umurci gabatar da lafiyar inshora da ake yi, da ta zama wajibi a dukkannin ma’aikatu da hukumomin gwammatin tarayya bisa tsari na dokar lafiyar inshora ta shekarar 2022 da ta.

A wata sanarwa da mai bai’wa shugaban shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar a ranar Larabar nan,shugaban ya umurci Sakataran gwamnatin tarayya da ya fitar da takardar sanarwa ga ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da su bi umurnin sanarwar cikin gaggawa.

Sanarwar ta ce umurnin ya hada da manyan bangarori biyar wadanda suka hada da ma’aikatan da suke karkashin hukumomin sa-kai da ke cikin tsarin inshora na taimakekeniyar lafiya.

Sannan an kuma umurci hukumar lafiyar inshora ta Kasa da ta kirkiri wani zaure na zamani domin ganin an bayar da shaidu saboda samun inganci a harkar.

A karshe sanarwar ta ce, umurnin da fadar shugaban kasa ta bayar zai fadada zuwa dukkanin inda ake da bukata, sannan ya kuma zamto ba sai sun biya komai daga aljihunsu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: