Kungiyar Likitoci mazauna babban birnin tarayya Abuja ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugabanta, Dr George Ebong ya fitar, tare da sauran membobin zartarwar kungiyar.

Likitocin mazauna Abuja sun bayyana tsarin kiwon lafiya a birnin a matsayin gazawar tsarin da ya dade tana ma bukatar gyara cikin gaggawa.

Ebong ya jaddada cewa likitoci a babban birnin tarayya Abuja na fuskantar matsananciyar matsin lamba, inda akai-akai aka rufe sassa da dama na bangaren.

Ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta gaggauta magance matsalolin da ke tasowa a fannin kiwon lafiya, yana mai gargadin cewa ci gaba da sakaci na iya haifar da rugujewar tsarin.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin da ta shiga batun cikin gaggawa a fannonin da suka hada da karancin ma’aikata, kayan aiki marasa amfani, rashin kyawun yanayin aiki, da alawus-alawus na ma’aikata.

Sannan ta kuma nuna damuwa game da rashin biyan albashi, jinkirin karin girma, da rashin biyan ma’aikatan da suka ci gaba, inda ta bukaci gwamnati da ta hanzarta yin aiki don bunkasa halin ma’aikatan kiwon lafiya tare da dawo da ingancin bangaren.

Sai dai a bangaren gwamnati Karamin ministan lafiya Dr Isaq Salako, ya bayyana kwarin gwiwar cewa tattaunawar da gwamnatin tarayya ke yi da kungiyar likitoci ta kasa za ta hana yajin aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: