Gwamnatin jihar Kano ta ayyana gobe Juma’a a matsayin ranar hutu a dukkan fadin Jihar, a ci gaba da gudanar da bukukuwan Maulidi, na tunawa da haihuwar Annabi Muhammad S,A,W.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake shirin fara gudanar da bikin Takutaha a birnin a ranar Asabar mai zuwa.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na Kano, Kwamrad Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu, gwamnatin ta bukaci al’ummar Jihar da su gudanar da bukukuwan lafiya, tare da bin koyarwar Manzon tsira Annabi muhammad Salahu alaihi wasalam.

Sannan sanarwar ta kuma bukaci al’ummar Jihar da su yi amfani da lokacin wajen gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya, da ci gaban jihar, dama Kasa baki daya, da kuma yin koyi da dabi’u da halaye da Manzon Allah Sallahu Alaihi wasallam.
