Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke wa Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, daya daga cikin kwamandojin kungiyar Ansaru, hukuncin daurin shekaru 15 a gidan gyaran hali.

Kotun ta yanke hukuncin ne a zaman da ta gudanar a yau Alhamis, bayan hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gurfanar da su.
A yayin zaman na yau, Usman ya amsa laifin da ake zarginsa da su, na mallakar makamai da ayyukan ta’addanci da kuma garkuwa da mutane.

Alkalin kotun Mai shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a hannun hukumar DSS har zuwa lokacin da za a gurfanar da shi kan wasu tuhume-tuhume 31 da hukumar ta gabatarwa da kotun.

A cikin tuhume-tuhume 32 da aka gabatarwa da kotun, Usman da mataimakinsa Mahmud Al-Nijeri, ana zarginsu da aikata ta’addanci a Najeriya a shekarar 2022 ta hanyar kai hare-hare a wasu sassan na Kasar.