Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta shigar na neman a gaggauta ci gaba da shari’ar wadanda ake zargi da hannu wajen kai harin bam a ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, Khalid Al-Barnawi da wasu mutane hudu a ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2011.

Hukumar ta gabatar da bukatar gaggauwan ne ta bakin lauyanta, Alex Iziyon, don sauraren karar kuma hukumar ta shirya don tabbatar da an yanke musu hukunci a kan lokaci.

Bayan gabatarwa da kotun takardar lauyoyin wadanda ake tuhuma ba su yi adawa da bukatar ba, inda za a bai’wa bangarorin damar kallon faifan bidiyo da hukumar ta DSS ta gabatar, bayan wasu daga cikin wadanda ake tuhumar sun musanta.

Mai shari’a Emeka Nwite ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Oktoba da 24 ga watan na Oktoba mai kamawa domin ci gaba da shari’ar.

Ana tuhumar Al-Barnawi ne bisa zargin ta’addanci tare da wasu da ake zargin ‘yan kungiyarsa ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: