Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta kama jabun magungunan zazzabin cizon sauro da kudinsu ya kai naira biliyan 1.2 a jihar Legas.

A wata sanarwa da NAFDAC ta fitar a yau Juma’a ta ce an kama magungunan ne a yankin Ilasa-Oshodi na jihar.
Acewarta ta kama katan 277 na jabun magungunan zazzabin cizon sauro, wadanda kudinsu ya kai sama da biliyan 1.2, a wani dakin ajiyar kaya dake unguwar Ilasa-Oshodi.

Magungunan wadanda aka boye a cikin kwalayen magani, an shigo da su ne ba bisa ka’ida ba daga wani kamfanin a kasar China.

Darakta Janar ta hukumar Mojisola Adeyeye, ta tabbatar da aniyar hukumar tare da cikakken goyon bayan fadar shugaban kasa da ma’aikatar lafiya ta tarayya, na kawar da jabun magunguna da marasa inganci daga Kasar.
Sannan ta ce kaman wani bangare ne na ci gaba da ayyukan NAFDAC a fadin kasar don kare lafiyar jama’a da kuma tabbatar da lafiya, magunguna masu inganci ne kawai ga ‘yan Kasa.