Bayan wata guda da rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta ceto wasu yara 14 da aka yi garkuwa da su zuwa jihar Anambra, an kuma ceto wasu yara biyar da aka sace daga jihar Borno a karamar hukumar Mubi ta jihar Adamawa.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya fitar a Lahadin nan, ya ce an sace yaran ne daga Maiduguri babban birnin jihar Borno, inda aka kai su Jihar ta Adamawa.
Sanarwar ta ce nasarar ta samu ne a jiya Asabar 13 ga watan nan na Satumba, a lokacin da aka ga yaran na gararan ba akan titi.

Sanarwar ta ce, yaran da aka ceto sun hada da Adamu Musa mai shekaru 16, Suleiman Idris mai shekaru 10, Suleiman Mohammed mai shekaru 11, Dauda Yahaya mai shekaru 11, da kuma Mohammed Alhassan mai shekaru 11, dukkansu mazauna garin Gwange ne a Maidugurin jihar Borno.

Sanarwar ta bayyana cewa, bincike ya nuna cewa wani Aliga Suleiman na Sabon Layi Gwange a Maiduguri, shi ne ya tafi da wadanda abin ya shafa daga Maiduguri ba bisa ka’ida ba.
Nguroje ya ce ana ci gaba da kokarin kama wanda ake zargin tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
