Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta sanya dokar ta-baci a fannin kiwon lafiya, biyo bayan nazari akan inganta harkokin kiwon lafiya a fadin Jihar.

Kwamishinan yada labarai na Elder Aniekan Umanah ne ya bayyana hakan, bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka yi a gidan gwamnatin Jihar da ke Uyo.
Ya ce za a sanya dokar ta-bacin ne bisa wasu muhimman umarni, kuma matakin, an tsara shi ne don hanzarta yin gyare-gyare da kuma samar da ingantaccen yanayi mai kyau na kiwon lafiya daidai da tsarin gwamna Umo Eno.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamna Sanata Akon Eyakenyi, Sakataren gwamnatin Jihar Shugaban ma’aikatan gwamnati, babban Mataimakin shugaban Kasa, kwamishinoni; da masu bayar da shawara na musamman.

A karkashin shirin za a kara inganta cibiyoyin kiwon lafiya a fadin jihar, yayin da aka sake bude daukar ma’aikatan lafiya.
Kwamishinan ya ce suna daukar ma’aikatan kiwon lafiya 2,000, gwamnan ya kuma bayar da umarnin yin garambawul a fannin horas da likitoci.
Majalisar ta bayar da umarnin inganta cibiyoyin horas da kiwon lafiya, da shigar da jami’an kiwon lafiya da horas da ma’aikatan lafiya, da kuma daukar ma’aikatan lafiya da suka yi ritaya.
Kwamishinan ya kuma ce gwamnan ya amince da karin kudirin kasafin kudi na Naira biliyan 695, wanda ya kai adadin kasafin na shekarar 2025 zuwa tiriliyan 1.65., daga cikin an ware Naira biliyan 125.6 don kashe kudade akai-akai, yayin da aka ware Naira biliyan 569.3 domin kashe kudi.
A cewar Umanah, karin kasafin kudin zai dauki nauyin tsare-tsare da dama da suka hada da aiwatar da sabon mafi karancin albashi, biyan alawus alawus ga ‘yan masu bautar Kasa, da ke aiki a ciki da wajen jihar, da shawo kan matsalar ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, da kuma kammala ayyukan da ake ci gaba da yi sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.
