Kungiyar SERAP ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da ta tantance tare da gurfanar da ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa da suka fara yakin neman zabe gabanin lokacin yakin neman zabe da doka ta amince Kasar.

A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Satumba nan, kuma ta aike wa shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu, kungiyar ta yi gargadin cewa za ta dauki matakin shari’a, idan har hukumar ta INEC ta gaza daukar mataki cikin kwanaki bakwai.
Sanarwar wadda mai magana da yawunta Kolawole Oluwadare, ya fitar yau Lahadi, SERAP ta bayyana yakin neman zaben da wuri a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, da kuma illa ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya da mulkin kasar.

A dai baya-bayan nan ne INEC ta bayyana damuwarta game da fara yakin neman zabe da wuri, inda ta yi nuni da cewa suna kawo cikas wajen bin diddigin kudaden yakin neman zaben.

Sai dai hukumar ta yi ta ce ba ta da hurumin sanya takunkumi akai, matakin da SERAP ta kalubalanta.
SERAP ta bukaci shugaban na INEC da ya bayyana ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa da suka sabawa kundin tsarin mulki, da tanadin doka, da ka’idojin kasa da kasa, wadanda suka haramta yakin neman zabe da wuri da kuma tabbatar da gurfanar da su a kotu da masu daukar nauyinsu.
SERAP ta kuma nemi da INEC ta dunga sanya ido sosai kan jam’iyyun siyasa da ke karya dokokin tsarin mulki wadanda suka haramta yakin neman zabe da wuri, da samar da kwararan tsare-tsaren da za su tafiyar da harkokin jam’iyyu da ‘yan siyasa dangane da yakin neman zabe da wuri a Kasar.
Kungiyar ta jaddada cewa INEC na da hurumi a tsarin mulki da doka, na ta hukunta laifukan zabe da suka hada da yakin neman zaben da wuri, wanda ya sabawa sashe na 94(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
