Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da aiwatar da harajin kyauta na kashi hudu cikin dari da hukumar kwastam ta Najeriya ta bullo da shi kan duk wasu kayayyaki da ake shigowa da su daga kasashen waje.

Matakin wanda Ministan Kudi Wale Edun ya sanar, ya biyo bayan damuwar da masu shigo da kaya, masana harkokin kasuwanci, da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antu ke yi game da illolin da harajin ke haifarwa.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga Satumban nan, kuma aka aika zuwa ga Kwanturola-Janar na Kwastam, Edun ya bayar da umarnin dakatar da harajin nan take.

Wasikar mai dauke da sanya hannun babban sakataren ayyuka na musamman a ma’aikatar kudi, Mista Raymond Omachi, ta bayyana cewa, an gudanar da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da masana da jami’an gwamnatin da abin ya shafa da dama, wadanda ra’ayoyinsu ya nuna cewa harajin zai kawo babbar illa ga kasuwanci da tattalin arzikin Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa masu ruwa da tsaki, musamman masu shigo da kaya da masu hada-hadar kasuwanci, sun sha gargadin cewa harajin zai kara tabarbarewar hauhawar farashin kayayyaki, da kuma kara farashin kayayyaki, tare da raunana karfin ci gaba a Najeriya, wanda kuma hakan zai dagula kokarin da ake yi na saukaka tsadar kasuwanci a kasar.

Ministan ya ce dakatarwar na da nufin samar da tsari da ci gaba da tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki da kuma yin nazari sosai, kan tsarin harajin da kuma tasiri na dogon lokaci kan tattalin arzikin kasar.

Idan ba a manta ba a watan Afrilun shekarar nan, Kwanturolan Hukumar Kwastam, Adeniyi, ya sanar da shirin sake dawo da harajin kashi hudu, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, akai.

Sai dai Ma’aikatar kudi ta fayyace cewa dakatarwar ba sokewa ba ce, amma ya zama dole don sa ke tantance illolin harajin, inda ta jaddada kudirin gwamnati na daidaita samar da kudaden shiga da bunkasar tattalin arziki.

Ma’aikatar Kudi ta kuma ce ta na fatan yin aiki kafada da kafada da Hukumar Kwastam, da dukkan bangarorin da abin ya shafa don samar da tsarin kudaden shiga mai inganci da daidaito, wanda ke tallafawa kudaden shiga na gwamnati ba tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci ko daidaita tattalin arziki ba.

Ana sa ran gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da suka hada da kungiyoyin kasuwanci, masu jigilar kaya, da masu shigo da kaya, don tsara tsarin adalci wanda ba zai wuce gona da iri ba.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: