Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya daga Kasar Faransa, bayan ya yanke hutun aikinsa kafin lokacin da aka tsara.

Shugaban ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da misalin karfe 6:50, na yammacin yau Talata, inda ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati.
Shugaban ya tafi kasar Faransa ne a ranar 4 ga Satumban nan, domin gudanar da wani bangare na hutunsa na shekara, kuma da farko an shirya zai yi kwanaki goma na aiki tsakanin Faransa da Birtaniya.

A wata sanarwa da Bayo Onanuga mai bai’wa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru ya fitar a jiya Litinin, ya ce shugaban zai koma Abuja a ranar Talata 16 ga Satumban nan domin ci gaba da aikinsa.

