Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, ta sake gurfanar da tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Apo, bisa zarginsa da damfarar kwangilar dala biliyan shida.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis,
Hukumar ta yi zargin cewa Agunloye, wanda ya rike mukamin minista a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003, a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayar da kwangilar gina tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawat 3,960 ta Mambila akan Gine-gine, Aiki da Canja wurin.

EFCC ta shaidawa kotun cewa kwangilar da aka bai’wa Kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Limited, an yi ta ne ba tare da wani tanadi na kasafin kudi ba.

Acewarta a wancen lokacin tsohon Ministan ya ki bin umarnin Shugaban kasa da aka yi bayan taron Majalisar zartarwa ta Tarayya, da aka yi a ranar 21 ga Mayun 2003, ta hanyar mikawa kamfanin wasika, tare da mika amincewar gwamnatin Tarayya kan kwangilar.
Mai gabatar da kara, wanda ya tuhumi wanda ake zargi da karbar Naira biliyan 3 daga kamfanin, inda aka dogara da takardun jabu don sauƙaƙe bayar da kwangilar.
Sai dai tsohon Ministan ya ce ba shi da laifi kan tuhume-tuhume bakwai da ake yi masa.
Daga bisani Lauyan mai gabatar da kara M.K Hussein ya nemi kotun ta ba shi rana don bai’wa shaida na uku a kan lamarin damar ci gaba da bayar da shaida.
Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Oktoban shekarar nan don ci gaba da shari’ar.
A baya dai kotun ta bayar da belin wanda ake kara kan kudi Naira miliyan 50 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.