Majalisar dokokin Najeriya ta yi kira da a janye duk wani daftarin da aka fitar a baya na bayar da kwangila a kasafin kudin shekarar 2025.

Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin fara aiwatar da babban kaso na kasafin kudi na shekarar 2025 na Naira Tiriliyan 23.9, kuma ana sa ran za a tsawaita har zuwa shekarar 2026.
An cimma matsayar ne a wata ganawa tsakanin kwamitin hadin gwiwa kan kasafin kudi da kungiyar tattalin arzikin shugaban kasa a majalisar dokokin kasar a yau Alhamis.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Kudi Wale Edun, Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Sanata Atiku Bagudu, Darakta Janar na ofishin kasafin kudi, Tanimu Yakubu, da Akanta-Janar na Tarayya Shamsudeen Ogunjimi.

An gudanar da zaman ne domin duba yadda kasafin kudin shekarar 2024 ya gudana, da kuma tantance yadda aka aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025 na Naira Tiriliyan 54.9.
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Abubakar Kabir Bichi, ya ce za a soke takardar da ma’aikatar kudi ta bayar na dakatar da bayar da kwangiloli har sai an fitar da AIE.
Ya kara da cewa za a fara aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025 nan take, tare da bayar da ikon kashe kudi na AIE a cikin kwanaki bakwai.
‘Yan majalisar sun kuma kara wa’adin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2024 zuwa watan Disamban shekarar nan, da kudurin da kwamitin hadin gwiwa karkashin jagorancin Sanata Adeola Olamilekan ya zartar.