Majalisar dokokin jihar Rivers ta bukaci gwamna Siminalayi Fubara da ya mika sunayen kwamishinoni ga majalisar domin tantancewa.

Majalisar karkashin jagorancin shugabanta, Martin Amaewhule, ta yi kiran ne a lokacin da suka koma zama a yau Alhamis, kasa da sa’o’i 24 bayan da shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya kawo karshen dokar ta-baci a jihar.
Sai dai duk da janye dokar ta bacin da shugaban ya yi a Jihar, gwamna Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu ba su isa gidan gwamnatin Jihar da ke Fatakwal ba har zuwa yammacin wannan rana.

Ya yi da a gefe guda daruruwan magoya bayan gwamnan a safiyar wannan rana suka taru a gidan gwamnatin Jihar, don tarbar gwamnan da mataimakinsa.
