A gobe Juma’a ne shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar babban birnin taraya Abuja, tare ziyartar Jihar Kaduna.

Mai magana da yawun shugaban na musamman kan yada labarai da dabaru Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa a yau Alhamis.

Ya ce Shugaba Tinubu zai je Jihar ta Kaduna ne halarci daurin auren Nasirudeen Yari da Safiyya Shehu Idris, inda Nasirudeen ya kasance da ne ga Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma Sanata Abdul’aziz Yari.

Sannan kuma shugaban zai kuma ziyarci Aisha Buhari, matar marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a gidanta da ke Kaduna.

Bayan kammala ziyarar shugaban zai koma Abuja.

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: