Kungiyar Likitoci ta kasa reshen babban birnin tarayya ta dakatar da yajin aikin da take yi.

Shugaban kungiyar George Ebong ne ya bayyana hakan ga Channels TV, ya ce ana sanya ran mambobin za su koma bakin aiki a ranar Litinin 22 ga watan Satumbanan.

Shugaban ya bayyana cewa dakatarwar ta biyo bayan tsoma bakin kwamitin majalisar dattawa mai kula da kananan hukumomin Abuja da sauran al’amura.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu ba a biya ko daya daga cikin bukatun kungiyar ba.

Ya kuma bayyana cewa kwamitin majalisar dattawa ya bai’wa kungiyar tabbacin ganawa da ministan babban birnin tarayya nan ba da dadewa ba, domin shawo kan matsalolin da suka dabaibaye su.

Kungiyar dai ta shiga yajin aikin ne a ranar Litinin din da ta gabata, bisa gaza biya mata bukatunta da gwamnati ta ki yi.

Daga cikin bukatun akwai gaza biyansu, albashi, daukar sabbin ma’aikatan, alawus-alawus da dai sauransu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: