Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce mutane uku ne suka mutu, yayin da akalla gidaje 1,415 ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Adamawa.

Hukumar ta bayana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru a ranar Talata, bayan da aka yi ruwan sama, inda ya shafi kananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu.

NEMA ta kara da cewa sama da mutane 40 ne suka samu raunuka, gonaki da muhimman ababen more rayuwa kuma ambaliyar ta lalata, tare da raba iyalai da matsugunnansu da kuma kawo cikas ga rayuwarsu.

Hukumar ta ce a wani binciken gaggawa da ofishinta na Yola ya gudanar, tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Adamawa ADSEMA, da masu ruwa da tsaki suka gudanar ya nuna cewa al’ummomi 13 ne lamarin ya shafa.
Hukumar ta ce a halin yanzu an tsugunar da waɗanda suka rasa matsugunansu a cikin ƴan gudun hijira, yayin da wasu kuma aka mayar da su sansanin da ake tsugunar da waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Girei.
NEMA ta ce wadanda abin ya shafa na bukatar taimakon gaggawa da ya hada da abinci, matsuguni, tallafin likitoci, da ruwa mai tsafta.
Hukumar ta yi kira ga mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su kasance cikin taka tsan-tsan tare da bin shawarwarin gargadi daga hukumomi, yayin da damina ke kara ƙarfi.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da yin aiki tare da ADSEMA, da kwamitocin gaggawa na cikin gida, da kuma sauran hukumomin jin kai domin dakile illolin iftila’i da kuma bayar da agajin akan lokaci ga mutanen da abin ya shafa.

