Jam’iyyar haɗaka ta ADC ta mayar da martani ga fadar shugaban kasa kan kalamanta na baya-bayan nan na cewa shugaban kasa Bola Tinubu ba shi da wani shiri na tsawaita wa’adin mulkinsa fiye da shekarar 2031, inda ta bayyana kalaman a matsayin rashin bin tsarin dimokradiyya.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa Malam Bolaji Abdullahi ya fitar, jam’iyyar ta tabbatar da cewa wa’adin shugaban kasa Tinubu zai kare ne a shekarar 2027, kuma jam’iyyar tana da yakinin cewa ‘yan Najeriya ba za su yi fatan kara wa’adinsa ko da na kwana guda ba.
Jam’iyyar ta ce duba da yawaitar ‘yan ta’adda da kashe-kashe da ake fama da su a fadin kasar nan, da yunwa da wahalhalun da ake fama da su a Ƙasar, tana mai cewa ya kamata shugaban kasa Tinubu ya yi shirin barin kasar nan a 2027.

Fadar shugaban kasa ta mayar da martanin ne dangane da kalaman tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufa’i na baya-bayan nan, cewa shugaba Bola Tinubu na da shirin zama shugaban kasa na dindindin.

ADC ta kara da cewa a halin yanzu a Ƙasar nan yan ta’adda, da ƴan fashi, da masu aikata laifuka, a halin yanzu na cin karansu babu babbaka ba tare da wani hukunci ba.
Sannan ta ce ana garkuwa da mutane da rana tsaka, al’ummar karkara na cikin fargaba, yayin da rashin tsaro ke ƙara tsananta, kuma gwamnati ba ta da niyya ko karfin dakatar da hakan.
Kazalika tattalin arziki kuwa yana cikin ruɗani, Naira ta durkushe, hauhawar farashin kayayyaki ya kau, yayin da kuma farashin kayan abinci ya ninku sau uku a sassan kasar nan.
