Uwargidan shugaban Ƙasa Bola Tinubu Oluremi Tinubu, ta tara sama da naira biliyan 20 domin aikin dakin karatu na Ƙasa da ke Abuja.

A farkon wannan watan ne uwargidan shugaban kasar ta yi kira ga masu hannu da shuni da su mayar da kyautuka na zagayowar ranar haihuwarta zuwa gudummawar da za a yi, domin ganin an kammala aikin dakin karatun na kasa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Uwargidan shugaban ta cika shekaru 65 a duniya, inda a wani sakon bidiyo da ta wallafa, ta bayyana cewa za ta sadaukar da ranar ga Allah da kuma wani abu da ta bayyana na kusa da zuciyarta, maimakon gudanar da wani gagarumin biki.

Acewarta ma’aikatar ilmi ta tarayya ce ke kula da ɗakin karatun a karkashinta.

Ta kara da cewa kammala ginin ɗakin karatun na Ƙasa zai zama wata babbar kyauta agareta
Da ta ke yiwa manema labarai karin haske a fadar shugaban Kasa Remi, ta ce ita mamba ce a kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ilmi, a lokacin da ta ke Majalisar, inda ta ce ma’aikatar ilmi ba ta iya gina ɗakin karatu na Ƙasa ba.

Ta kara da cewa, ba ta ji dadin yadda har yanzu ba a kammala dakin karatun ba, da aka fara a zamanin tsohuwar gwamnatin Shehu Shagari ba.

Ta ce ya zuwa yanzu ‘yan Najeriya sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 20, sannan sauran na ci gaba da shigowa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: