Kwamitin da ke kula da harkokin kudi na babban bankin Najeriya CBN ya rage yawan kudin ruwa na kasar zuwa kashi 27.00 cikin 100, wanda shi ne karon farko a shekarar 2025, bayan dakatarwa sau uku a jere.

Gwamnan babban bankin na CBN, Olayemi Cardoso ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a yau Talata a Abuja bayan kammala taron MPC karo na 302 da aka gudanar a ranakun 22 da 23 ga watan Satumba, inda dukkan mambobin kwamitin 12 suka halarci taron.
Cardoso ya ce kwamitin ya yanke shawarar rage yawan Manufofin Kudi da kashi 50, haɓaka buƙatun Kuɗi na Bankunan kasuwanci zuwa kashi 45 cikin 100, yayin da suke riƙe da na bankunan yan kasuwa a kashi 16 cikin 100, da gabatar da TSA na kashi 75 cikin 100 na CRR akan sassan da ba na kasuwanci ba.

Har ila yau ya ce raguwar adadin ya dogara ne akan ci gaba da raguwar hauhawar farashin kayayyaki da aka samu a cikin watanni biyar da suka gabata, hasashen raguwar hauhawar farashin kayayyaki a 2025, da kuma bukatar tallafawa kokarin farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Kwamitin ya lura cewa hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 20.12 cikin 100 a watan Agusta daga kashi 21.88 a watan Yuli, yayin da hauhawar farashin abinci ya ragu zuwa kashi 21.87 bisa 100 daga kashi 22.74 cikin dari.
Hakanan kuma hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa kashi 20.33 daga kashi 21.33 cikin 100 a wannan lokacin, inda a wata-wata kuma hauhawar farashin kayayyaki ya ragu sosai zuwa kashi 0.74 a cikin watan Agusta idan aka kwatanta da kashi 1.99 a watan Yuli.
Kwamitin ya yaba da kokarin gwamnatin Tarayya na inganta tsaro a yankunan da ake hako mai, inda ya jaddada cewa ci gaba da bunkasar noma zai taimaka wajen samun karbuwa daga waje da kuma daidaiton kudaden waje.
Sannan an sake shirya taron na MPC na gaba a ranakun 24 da 25 ga watan Nuwamban shekarar nan.
