Gwamnan jihar Abia Alex Otti, ya yi wa majalisar zartarwar jihar garambawul, tare da kara wasu kwamishinoni biyu da kuma mai bayar da shawara na musamman guda daya.

Kwamishinonin sun hada da Salome Obiukwu, wanda yanzu ya karbi mukamin kwamishinan kasuwanci, sai Chiemela Uzoije a matsayin kwamishinan gidaje, da Christian Enweremadu a matsayin mai bai’wa gwamna shawara na musamman kan harkokin noma.
Da yake jawabi yayin rantsarwar da su a gidan gwamnatin Jihar a yau Talata, Otti wanda ya bayyana gyare-gyaren a majalisar, ya ce tsohon kwamishinan ciniki da kasuwanci, Kingsley Nwokocha, yanzu ya koma kwamishinan kwadago da samar da kayayyaki.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa an raba ma’aikatar filaye da gidaje gida biyu domin inganta aikinta, inda ya ce Chaka Chukwumerije ne kwamishinan filaye.

Otti ya bayyana nadin a matsayin wani bangare na dabarun gwamnatinsa, na samar da sabbin dabaru lokaci-lokaci don inganta fadada ayyukan gwamnatinsa.
Kazalika ya yi amfani da damar wajen bayyana wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin watanni 28 da suka gabata, wadanda suka hada da inganta ababen more rayuwa a hanyoyi, tsaro, ilimi, da kuma kiwon lafiya.
Sannan ya ta wadanda aka nada murna, tare da jaddada musu manufofin gwamnatinsa na rashin cin hanci da rashawa, da kuma gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta wadanda aka kama da laifi.
Otti ya jaddada bukatar sabbin jami’an da su gaggauta aiwatar da ayyukansu, yana mai jaddada cewa nadin ya fara aiki ne nan take.
