Majalisar dokoki ta Ƙasa ta dage ci gaba da zamanta na tsawon makonni biyu.

Tun da fari Majalisar ta shirya za ta koma bakin aiki ne a yau 23 ga watan Satumba, inda ta dage komawar zuwa ranar 7 ga watan Oktoba mai kamawa.
Hakan na kunshe a cikin wata wasika da aka aikewa daukacin ‘yan majalisar wadda magatakardan ta Kamoru Ogunlana ya aike musu.

A cikin sanarwar Ogunlana ya bukaci dukkan Sanatoci da ƴan Majalisun wakilai da su kula da sabuwar ranar, tare da tsara jadawalin su yadda ya kamata.

Ogunlana ya ce shugabannin majalisun biyu ne suka bashi umarnin sanarwa da ‘yan majalisar karin hutun dage zaman majalisar, da tun farko aka shirya gudanarwa a yau Talata, tare da mayar dashi 7 ga watan na Oktoba 2025.
Sai dai sanarwar ta ce kwamitocin Majalisar za su ci gaba da gudanar da ayyukansu.
