Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike, da ya gaggauta fara gina dakunan kwanan dalibai biyu, inda kowannen zai kasance da dakuna 300 a makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya da ke Abuja.

Shugaban ya kuma bayar da umarnin gina hanyar da za ta hada Sakatariyar Benchers da ke yankin Jabi da Jami’ar Nile.

Babban mataimaki na musamman ga Ministan babban birnin tarayya Abuja kan harkokin sadarwa da kafafen sadarwa na zamani Lere Olayinka, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, inda ya ce za a gudanar da ayyukan ne a cikin gaggawa.

Ya bayyana cewa za a gina dakunan kwanan dalibai mata guda daya, dana maza guda daya wanda kowannensu zai iya daukar mutane 300 domin samar da wurin kwana ga daliban makarantar.

Olayinka ya kara da cewa hanyar idan aka kammala ta, za ta rage cunkoson ababen hawa akan hanyar zuwa babban ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: