Gwamnatin jihar Kebbi ta jaddada kudirinta na karfafa gwiwar jami’an tsaro a yakin da suke yi da ‘yan bindiga da ƴan ta’adda a fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai da al’adu na Jihar Alhaji Yakubu Birnin Kebbi ne bayyana hakan a Juma’ar nan, a lokacin da ya karbi bakuncin daraktan yada labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Isma’il Gusau, a ziyarar ban girma da ya kai a Jihar Kebbi.

Ya bayyana cewa tun hawan gwamnan Jihar Nasir Idris mulki shekaru biyu da suka gabata, gwamnan ya ci gaba da bayar da tallafin kayan aiki, alawus-alawus da kuma bayanan sirri ga jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa gwamnatin za ta ci gaba da fadada irin wannan tallafin.

Sannan ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin jami’an tsaro a Jihar, sun samu karin nasarori akan masu aikata laifuka a fadin Jihar.

Kwamishinan ya ce su na bukatar hedkwatar tsaro ta shirya wani taro na musamman, wanda zai hada sarakunan gargajiya, malaman addinai, shugabannin al’umma, kungiyoyin matasa, da sauran masu ruwa da tsaki, ya ce irin wannan haɗin gwiwar za ta ƙarfafa musayar bayanan sirri, da kuma kara kaimi ga al’umma baki ɗaya a ayyukan tsaro.

Ya bayar da tabbacin cewa ma’aikatarsa a shirye take ta hada kai da ma’aikatar yada labarai ta tsaro, don gudanar da taron, da kuma hada kan shugabannin kasa don tallafawa ayyukan samar da zaman lafiya.

Anasa bangaren Birgediya Tukur Gusau, ya ce ya kai ziyarar ne domin duba yadda ake ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin sojoji da ‘yan jarida, wajen karfafa huldar soja da jama’a a Jihar Kebbi da ma yankin Arewa maso Yamma.

Ya kuma yabawa gwamnan Nasir Idris bisa goyon bayan da yake bai’wa rundunar soji, inda acewarsa na taimakawa matuka wajen samun nasarar dawo da kwanciyar hankali ga al’ummomin da rashin tsaro ya shafa.

Bugu da kari ya kuma mika godiyar babban hafsan tsaron kasa Janar Christopher Musa, ga gwamnatin Kebbi bisa jajircewar da take yi na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a lungu da sako na Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: