Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa mawuyacin halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a halin yanzu ya zama tarihi.

Ya bayyana haka ne a Juma’ar nan, a dakin taro na Mapo da ke garin Ibadan babban birnin jihar Oyo, a lokacin bikin nadin sarautar mai martaba Oba Adewolu Ladoja mai dimbin tarihi, Olubadan na 44.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa a halin yanzu ƴan Najeriya na ci gaba da darawa, bayan halin matsi da tattalin arzikin ke ciki, ya zama tarihi.

Acewarsa halin matsi da aka shiga a Ƙasar, sun yi musu radadi, inda ya ce a yanzu tattalin arzikin ya ɗaiɗaita.

Shugaba Tinubu ya kuma taya murna ga sabon Sarki, tare da yin fatan alkhairi ga al’ummar Kasa, bisa jajircewar da suka nuna.
Sabon arkin ya kasance tsohon gwamnan jihar ta Oyo, wanda ya hau karagar mulki bayan shekaru 32, na ci gaba ta hanyar tsarin sarautar gargajiya a Jihar.
