Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya bukaci majalisar dokokin kasar nan da ta kafa wata kotu ta musamman da za ta dunga gudanar da shari’ar cin hanci da rashawa a Najeriya.

Sule ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a, a yayin bikin kaddamar da faretin ’yan sanda kashi na goma da kuma kashi na Bakwai na hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, wanda aka gudanar a kwalejin horaswa na rundunar ‘yan sanda ta Ƙasa da ke Akwanga a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa shari’ar cin hanci da rashawa a kasar nan, kan dauki tsawon lokaci kafin a kareta, wanda hakan ke kawo cikas ga yaki da matsalar.

A cewarsa, ba za a dauki Najeriya da muhimmanci a duniya ba, har sai ta magance matsalolin cin hanci da rashawa a fadin Ƙasar.

Gwamnan ya kuma yabawa Shugaban Hukumar EFCC na Ƙasa Ola Olukoyede, da Shugaba Bola Tinubu, bisa jajircewar da suka yi na kokarin ganin an magance matsalar a Ƙasar.
Yayin da yake yabawa da kalubalen da ake fuskanta na magance miyagun laifuka, musamman cin hanci da rashawa, gwamna Sule ya yabawa sabbin jami’an da aka yaye bisa nuna da’a, juriya, da jajircewa, ya kara da cewa halayensu na nuni da fata ga makoma mai kyau a kasar.
Kazalika ya bukaci jami’an da su sadaukar da kansu wajen bautawa Ƙasar nan.
A nasa jawabin Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya jaddada kudirin hukumar na kawar da cin hanci da rashawa a karkashin shugabancinsa.
Ya kuma bukaci sabbin jami’an da su jajirce wajen samun nasarorin hukumar, yana mai jaddada dimbin jarin da Najeriya ta samu wajen horas da su.
