Hukumar jindadin alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana sabon farashin maniyyata aikin hajjin bana na shekarar 2026.

Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne hukumar ta sanya Naira miliyan 8.5 a matsayin kudin tafiyar da aikin Hajji na shekarar 2026, har zuwa lokacin da za a bayyana kudin.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce maniyyatan da suka fito daga Jihohin Yobe, Borno, Adamawa da Taraba za su biya Naira miliyan 8,118,33.67, yayin da wadanda ke sauran jihohin Arewa za su biya Naira miliyan 8,244,813.67.

Sai dai wadanda ke jihohin Kudu za su biya Naira miliyan 8,561,013.67.

Sanarwar ta bayyana cewa an cimma farashin ne bayan tuntubar da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin kungiyoyi na Jihohi da kuma samun amincewar gwamnatin Tarayya.
Shugaban Hukumar na Kasa Farfesa Abdullahi Sale Usman ya bayyana cewa idan aka kwatanta da abin da aka bayar a shekarar da ta gabata, a bana kowane maniyyaci zai biya matsakaita akan Naira dubu dari biyu.
A halin yanzu dai tuni tawagar NAHCON da ke kasar Saudiyya sun gana, tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar da kamfanin samar da aikin Hajji na shekarar 2026 Mashareeq Al-Zahabiyya da kuma Kamfanin Sufuri Daleel Al-Ma’aleem.
Ya bukaci dukkan maniyyatan da su kammala biyansu kadadensu kafin ranar 31 ga watan Disamba shekarar nan.
