Jam’iyyar PDP reshen jihar Legas ta yi watsi da wani taro, da ake zargin wani bangare da ke goyon bayan tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Olabode George ne suka shirya.

Shugaban jam’iyyar a jihar Philip Aivoji ne ya bayyanawa manema labarai a ranar Asabar a yayin wani taron manema labarai.
Ya ce taron ya kasance mara inganci, sabawa doka kuma ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa wa’adin shugaban na yanzu ya kasance har zuwa watan Maris 2026.

Ya ce sashi na 25 (1) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP, ya ce shugaban jam’iyyar da aka sani ne kadai zai iya jagorantar irin wannan taron.

Acewarsa wannan taron zai kara dagula rarrabuwar kawuna a jam’iyyar, inda ya ce mambobin jam’iyyar sun nesanta kansu daga taron, wanda aka yi gaggawar aiwatar da shi don biyan bukatar wasu ’yan jam’iyyar da son rai da cin hanci da rashawa da ‘ya’yan jam’iyyar suka yi.
Ya yi gargadin cewa mambobi masu biyayya sun riga sun yi barazanar ficewa daga jam’iyyar matukar ba a magance irin wannan ba.