Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya bukaci sabbin zababbun mambobin jam’iyyar PDP da su samar da hadin kai a cikin jam’iyyar yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zabe na 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi a yau Asabar a garin Yola, bayan taron zaben sabbin shugabannin jam’iyyar a jihar, gwamnan ya ce sakamakon zaɓen na nuna kyakkyawan fata ga jam’iyyar PDP a 2027.

Ya ce sun shirya tsaf don ganin sun sace karbe ragamar jihar a 2027 mai zuwa.

Gwamnan ya bukaci sabbin shugabannin zartarwar da su yi aiki tukuru wajen hada kan sabbi da wadanda suke da su wuri guda domin ganin jam’iyyar ta dawo da aikin ta.

Sabon shugaban jam’iyyar na jihar Alhaji Hamza Madagali wanda a baya ya taba zama sakataren jam’iyyar, ya yabawa wakilan da suka ba shi shugabancin jam’iyyar a jihar.

Ya kuma tabbatar wa ‘ya’yan jam’iyyar PDP cewa zai yi aiki tukuru domin ganin jam’iyyar ta ci gaba da rike jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: