Rundunar ƴan sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da hallaka ƴan ta’addan Lakurawa uku a wata musayar wuta da suka yi wutar a karamar hukumar Dandi.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Jihar, Nafi’u Abubakar ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a.

Ya ce jami’an yan sandan na shiyar kamba ne suka samu nasarar a yayin musayar wutar, a lokacin da wasu gungun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Lakurawa ne suka kai hari kauyen Gorun Yamma.

Acewarsa lamarin ya faru ne a ranar juma’a 3 ga watan oktoban nan, bayan samun bayanan sirri, inda Jami’in ɗan sanda na shiyar kamba Muhammad lawal, ya haɗa kan jami’an ƴan sanda da ƴan sa-kai zuwa wuri.

Da zuwan haɗin gwiwar jami’an tsaro sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan na dogon lokaci, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar uku daga cikin ƴan Lakurawan, yayin da wasu suka tsere zuwa cikin dajin dauke da raunika a jikin su.

Kazalika an gano wata jar mota kirar Honda mara rijista, wadda ake kira da boko-haram a yayi faruwar lamarin.

Yayin da yake yabawa aikin yan sandan, kwamishinan yan sandan Jihar ta Kebbi Bello Sani, ya yabawa jajircewar ‘yan sandan da ke Kamba, inda ya ce daukar matakin gaggawa da jami’an suka yi, ya dakile mummunan harin da ƴan ta’addan suka kai kan mazauna yankin da ba su ji ba ba su gani ba.

Kwamishinan ya bayar da umarnin mika karar zuwa sashin binciken manyan laifuka na Jihar domin ci gaba da bincike.

Akarshe ya kuma tabbatarwa da mazauna yankin kudurin rundunar na kawar da munanan laifuka a jihar, yayin da ya bukaci al’umma da su yi taka tsan-tsan, tare da bayar da bayanai akan lokaci ga jami’an tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: