Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya ce ba za a iya magance matsalar tsaro ba har sai an samu haɗin kai tsakanin ƴan Najeriya.

Janar Musa ya bayyana haka ne yau Juma’a ƙaddamar da wani littafi da tsohon hafsan tsaron Najeriya Lucky Irabo ya rubuta.

Ya ce matakin da soji ke ɗauka ba zai kawo ƙarshen Boko Haram ba har sai ƴan Najeriya sun haɗa kansu.
A cewarsa rawar da soji za su taka a ciki ba ta fi kaso 25 zuwa 30 ba.

Ya ce iya kwacewa da fahimtarsa matsalar ba wai soji ne kaɗai ke da alhakin kawo ƙarshenta ba, har sai jama’a sun haɗa kai har a kai ga nasara.

Ya ce matuƙar mutane ba za su so junansu ba kuma ba sa kallon kansu a matsayin yan uwa to matsalar za ta ci gaba da faruwa ne ba za a iya kawo karshenta ba.

Ya ce ba tsafi ba ne amma dole in har a na son a kawo karshen matsalar sai an so juna kamar yan uwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: