Tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka na kai ziyara Jihar Filato a jiya Asabar domin halartar jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa Farfesa Nentawe Yilwatda.

Alhaji Atiku ya bayyana hakan ne ta cikin wata wallafa da ya fitar a jiya Asanbar, ya ce mai makon shugaban ya kai ziyarar jaje ga al’ummar da rashin tsaro ya shafa, amma ya tafi wani gurin na daban.

Atiku ya bayyana ziyarar a matsayin jana’izar siyasa wanda ta bai’wa shugaban damar gudanar da biki da murna, tare da jiga-jigan jam’iyyarsa.
Acewar Alhaji Atiku a daidai lokacin da yankuna da dama na kasar nan ke fama da matsalar rashin tsaro da ke haifar da asarar dubban rayukan mutanen da ba su ji ba su gani ba, abin takaici ne matuka yadda shugaba Bola Tinubu bai ga dacewar ya ziyarci Jihohin da abin ya shafa ba don jajanta wa ‘yan kasar da ke cikin mawuyacin hali.
Atiku ya kuma bayyana cewa matakin da shugaban kasar ya dauka na halartar jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, hakan ya nuna halin ko in kula ga wadanda matsalar tsaro ta shafa a wasu yankunan kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: