Hukumar kare fararen hula ta NSCDC a Jihar Neja ta gurfanar da wasu mutane shida da ake zargi da laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a gaban kotu a wani samame da ta kai cikin dare.

Kwamandan hukumar a Jihar Suberu Aniviye ne ya bayyana hakan a hedkwatar hukumar da ke Minna, ya ce an kama mutanen ne da misalin karfe 12:00 na dare, a lokacin da ma’aikatan hakar ma’adanai suka samu sahihin bayanan sirri game da ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da suke gudanar da ayyuka.

Acewarsa bayan samun bayanan hukumar ta dauki matakin gaggawa, inda ta kama mutane shida a wurin, tare da babura tara da wasu kayan aiki da suke amfani da su wajen aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Ya bayyana cewa gwamna Muhammad Umaru Bago ya sanya hannun jari mai yawa a ayyukan samar da ababen more rayuwa a Jihar, kamar tituna da sauransu, wanda aka samu daga albarkatun jihar, ya ce a don haka ba za su zuba idanu ba wasu tsirarun mutane su dunga hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Kwamandan ya nanata kudurin hukumar na dakile ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar, inda ya yi gargadi ga masu aikata laifuka da su fice daga jihar ta Neja ko kuma su fuskanci hukuncin doka.

Ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, da masu ruwa da tsaki na al’umma da su tallafa wa hukumar ta hanyar wayar da kan al’ummarsu tun daga tushe.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: