Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana aniyar sake mayar da wasu mutanen yankuna uku da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a garin Banki da ke karamar hukumar Bama a Jihar.

Gwamnan wanda ya je Banki, inda ‘yan ta’addan suka kai hari a barikin sojoji da kan mutanen gari, a ranar Lahadi, ya jajantawa mazauna garin, tare da yabawa da juriyarsu.
Ya kara da cewa bai kamata su bar miyagun ƴan ta’addan su raba garin da kasuwanci da tattalin arzikinsa da ke bunkasa ba, inda ya tabbatar da cewa ƴan ta’addan ba za su yi nasara ba.

Kazalika ya ce za su karfafa tsaro a gari mai iyaka, kuma za mu tallafawa matasa masu aikin sa-kai, da mafarauta, da ƴan banga, don kara karfafa yanki.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa za a aiwatar da tsauraran matakan tsaro, domin kare garin daga hare-haren mayakan Boko Haram.
A ci gaba da shirinsa na farfado da wadanda rikicin boko-haram ya dai-daita kuwa, gwamnan ya kuma bayyana shirin sake tsugunar da al’ummar Kumshe, Tarmu’a da kuma Bula Yobe a karamar hukumar Bama, yana mai cewa mutane sun cancanci yin rayuwa mai mutunci, inda suka himmatu wajen ganin sun tabbatar da walwala da jindadinsu.
Zulum ya tabbatar da cewa an fara aikin gyaran hanyar Banki, inda tuni aka tura manyan motoci 30 domin gyara hanyar da ta lalace.
Ya yi kira ga al’umma musamman matasa da su tashi tsaye wajen gudanar da rijistar masu kada kuri’a domin ci gaban al’umma.
Hakazalika, gwamna Zulum ya kuma yi jawabi ga ‘yan kasuwa da ke kasuwar Banki, inda ya bukace su da su kiyaye, tare da bai’wa jami’an tsaro hadin kai domin samun dauwamammen zaman lafiya a yankin.