Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da nasarar kama masu aikata laifuka a fadin Jihar, inda ta kama wasu mutane 153 da ake zargi, tare da kama miyagun kwayoyi, kudade, da babura.

Mai magana da yawun rundunar Lawal Shisu Adam ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a garin Dutse.
A cewar sanarwar sun gudanar da aikin ne, da dukkan sassan ƴan sanda 42 da ke Jihar, inda aka tarwatsa maboyar ƴan ta’adda, da masu hada-hadar miyagun kwayoyi, a kokarin da suke yi na dakile aikata laifuka a Jihar.

Kakakin ya tabbatar da cewa kamen na da nasaba da laifuka da suka hada da safarar miyagun kwayoyi, mallakar haramtattun kayayyaki, da sauran wasu laifukan masu alaka.

Ya ce sun kwato miyagun kwayoyi masu tarin yawa daga hannun masu laifin, inda aka gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotu biyo bayan binciken da aka gudanar.
Sannan ya bukaci mazauna Jihar, da su ci gaba da bai’wa jami’an hadin kai, da bayanan sirri, a kokarin da suke ci gaba da yi na kawar da batagari a dukkan lungu da sako na fadin Jihar.
Akarshe rundunar ta gargadi masu aikata laifuka da su daina ko kuma su fuskanci hukuncin, tare da yin alkawarin ci gaba da hada karfi da karfe da al’umma wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.