Hukumar hana fasa kauri ta Ƙasa Kwastam reshen yankin Seme ta ce ta kama wasu haramtattun kayayyaki da suka hada da haramtattun kwayoyi da kuma fulawa da wa’adin amfani da ita ya kare daga kasar Masar, wanda kudinsu ya kai Naira biliyan 1.99 a tsakanin 1 ga watan Satumba zuwa 9 ga Oktoban nan, a kan hanyar Legas zuwa Abidjan.

Kwanturolan Hukumar Kwastam Wale Adenuga ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, a lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Ya ce fulawar da ta wa’adin amfani da ita ya kare an kama buhunhuna 10,000 da kudin harajin ta ya kai Naira biliyan 1.2, inda aka boye a cikin manyan motoci biyar.

Adenuga ya bayyana cewa, kayyakin da wa’adin amfaninsu ya kare nada matukar hadari ga lafiyar al’umma, da ka iya haifar da da cututtuka, matukar suka shiga kasuwanni.

Iyakar Seme da ke Badagry a jihar Legas, na daya daga cikin kan iyakokin Najeriya mafi yawan hada-hada da kuma kan iyakokin wasu kasashe.
Acewarsa a lokacin da jami’an suka gudanar da bincike, sun kama buhunan tabar wiwi 1,104 da tramadol 120, inda ya kara da cewa an mika wasu mutane biyu ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA domin gudanar da bincike.
Sauran kayayyakin da aka kama sun hada da buhunan shinkafa ‘yar kasar waje guda 2,043 mai nauyin kilogiram 50, da kayan sawa 150, kwalaben maganin tari na DSP 169 da codeine, da motoci biyar da aka yi amfani da su.
Ya kuma bayyana fasa-kwaurin a matsayin tabarbarewar tattalin arziki da ke hana al’ummar kasa samun muhimman kudaden shiga, da kuma jefa rayuwar al’umma cikin hadari, yana mai jaddada cewa idan aka karkatar da albarkatun kasa zuwa wata hanya hakan ka iya bai’wa kananan masana’antu da matsakaitan sana’oi karfi da kuma samar da ayyukan yi.